Chapter 8
Chapter 8
maki su i will draw You into my feet" yana fadin hakan ya juya a hankali yana tafiya cike da gadara yana doro yana tokare baya da kafada. Wani gigitaccen qara ta kwantsama "Adeel Na tsane ka!!!" Hankade mata kafadarsa yayi irin ko a jikinsa din nan ya dage kai ya bar wajen. Oum Aphnan 09065990265 [6/27, 1:09 PM] Chuchu👻: Zaune Yusrah take a falo ta rafka tagumi tana kallon joy prime da suke nuna latest waqoqin turanci wanda sukayi trending ,amma rabin hankalinta ne ke wajen sauran kuwa tana tunanin yanda rayuwa yake mata atishawan Quda ne.gabdaa ta koma rayuwar abaya en abayoyinta kadai take sawa don bazata iya sa kayan matacciya ba ,gabadaya ta sukurkuce gayunta ya ragu. Cikin gadara ya shigo falon ya kakare a gabanta ta yanda bazata iya kallon tv din ba kuma .siririn tsaki taja ciki² "Ina fatan kasan dai kai You Are not a transparent da zaka tsaya mun a gaba kuma in iya kallon abinda nike kallo" Bai kula ta ba yasa hannu ya dauki remote din tvn ya sauya zuwa tashan qwallon qafa,ya maida remote din ya aje a inda ya dauka . A fusace ta dauka remote din ta sake sauya channel din . "Ke idan kallon shashashn tashan nan kike son kallo tashi kije upstairs akwai Tv sai ki kalla a can" "Anan nike son kalla ,kai kaje saman mana" "Ki tashi ki bar wajen nan this is my living room muna da set din Tv guda goma sha biyu ne a gidan nan don haka kije ki kallonki a ko'ina Amma ki fita a nan...ina fatan kinsan gidan nan da abinda suke ciki mallaki na ne " Wani irin dariyar qasa qasa tayi masa kawai ta harde qafa daya kan daya . "Excuse you🤨😎😏Wai magana kake yi? Wannan wani yare kenan ? Naji Sam bai mun kama da yaren mutane ba" "Humm magana ake ta arziki i mean dukiya ba na matalauta ba irinku" Sosai maganarsa ya soya mata rai take anan idanuwarta suka sauya sukayi jaaa. Gyara zama tayi ta dago tana kallonsa "Kasan menene? Nagartaccen namiji ,I mean isasshen mijin aure ba ya taba cin zarafin matarsa bare har ya ringa zaginta yana mata gorin arziki ,amma fa ga wanda ya gaji arzikin ba wanda yayi hayen sa ba...amma kai dai kam hmmm☹️" Dariya ya soma qyaqyata mata har yana duqewa wannan yasa ta dago gamida tattare giran sama da qasa tana binsa da kallon mamaki. Cikin dariya yake bata amsa "wai dama ke kallon mace kike ma kanki? Oh above all matata? Hummm ai wannan matsayin na matata ce kuma kin kashe ta" zumbur ta mike tana gyara zaman rigarta. "Kasan menene bazan tsaya ina musayar miyau da kai ba ,you're just a rediculous coward wanda ya dauki cin zarafin mace ado 🙌gorin Arziki abin tinkaho...saidai bari kaji ,ba'a haifeni don a taka Ni ba kuma wallahi ina maka kyakkyawar albishir da cewa har abada nafi qarfin kayi over shadowing dina" ta qare magana tana banbanka masa harara. "Dallah yimun shiru da kucakin turancin ki sam ke bagidajiya ce turancin ma baki iya ba " Dariya ta fashe dashi tana tafa masa hannu "Nagode Allah kaji ko ,a hakan kake gane Yaren bagidajiyar kuma daqiqiyar har kana musu da ita ,kai ina wayewan naka yake wallahi kai matsolo ne na raina maka aji....." Knock knock knock Aka fara dukan kofar dakin daga waje. Da sauri yaje ya bude kofar wata hamshaqiyar macece ta shigo mai manyan mazaunni fara sol tana janye da trolley na matafiya . Yusrah kallon er cakulin jikinta tayi kana ta juya ta kalli almighty body din wannan bakuwar ,kawai sai ta harde hannu a qirji tana kallon ta. "Assalamu alaikum ina kwana ranka ya dade" "Barka da zuwa" cike da fara'a ta masa godiya kana ta daga hannu tace "Hiii Yusrah🤩 " Tattare giran sama da qasa tayi kana ta amsa da "waye ke" "Oh😃sunana Zuby(ina fatan dai kun tuna zuby kwartuwan Major a guess inn) Sabuwar malaman ki Yes your new teacher!" Wani miyau ne taji ya sarke mata maqoshi qiris ya rage ta qware . "Oh ban gane ba kikace kece wane dina?😂😡?" Yar ma yusra tayi da trolley din kayanta a tsakiyar falon "Kinaji maza biyoni da akwatina saman bene bari in dan kintsa ,shower up sai muyi magana " ta wuce cakas cakas tana juya mata mazaunai,shikuma yabi bayanta kamar wani shashasha suka wuce suna kwasan dariya "Oh kin dawo daga Dubai din kenan ,ban tsammanin zaki dawo da wirwuri hakan ba ,muje ki fada mun how was your trip" Oum Aphnan 09065990265 [6/28, 3:27 PM] Chuchu👻: Washegari yusra ta ɗan sha gayunta tana kwance akan resting chair din falonta na sama ,kunnenta maqale da bluetooth tana miming waqan nicki minaj a hankali .a saman kanta ta jiyo zuby na kwarara mata kira "Yusrah! Ke Yusrah" A nutse ta zare earpod din kunnenta guda daya tana kallonta Ba tare da tace mata kanzil ba . Zuby watsa takardun hannun ta da biro tayi akan table din gabansu ta samu kujeran kusa da ita ta zauna tana gyara zaman matsatsen rigar jikinta da ya fallasa asiri manyan boobs dinta ta v-neck din rigarta. "Excuse me yanzu lokacin karatunki yayi " Galala tayi mata da baki kamar goluwa tana mamakin abinda wannan zata koya mata a haka dinta wanda ko bata qwanqwasata ba zata iya assesing ilimin dake cikin kwanyarta. A sama taji tana mata introduction "wannan aikin koyar da gyaran hali ne,zan koya maki yanda ake magana ,yanda ake tafiyan ɗaa ,yanda ake gaisuwa da maida ma na gaba dake magana ,ke harma da yanda ake gyaran gida da girki.....yanzu dai da farko zan fara da tambayar ki.....Menene kika fahimta da kalmar *LADABI*?" Cikin gatsali da rashin daukan abu da muhimmanci Yusrah ta fara mata magana "Kin tabbatar kin ko cancanci wannan position din? Nifa kallon jahila na gasken gaske nike maki? Kin kalli suturan jikinki kuwa? Irin na kilakin nan en good evening masu neman maza su dauke su su cisu over night a siya masu indomie da qwai ko gasasshen kifi in sunci mugun sa'a a basu gasashen kaza da rufaida yoghourt safe in yayi a basu dubu biyu su gaida gida.....fada mun anya ke din ba irinsu ba ne" Gabadaya zuby ji tayi an gama muzantata. "Ban fahimce ki ba ! Ki natsu kina jina ko? Bazan dauki duk wani nau'in rashin da'a daga wajenki ba...ki saka nutsuwarki duka anan wannan shine job dina " Caɓe mata baki tayi gamida dage mata giran sama😏🤨 "Ok fadamun bisa qiyasi bisa dari ,matakin nawa zaki ba kanki na wannan fitsaran taki...?" Ba tare da yusra taji komai ba ta ɗan dafe kai kamar mai tunani "uhmmm Daidai dana Uwarki!!!😳 Hahahaha😂" Dafe qirji zuby tayi ta maza ta gyara zamanta tana duddulo mata ido cike da ɓacin rai ita kuwa yusra sai dariya take tana wasa da ƴan yatsun hannunta tamkar batayi komai ba "Kina da hankali kuwa? Ni kike zagi?😡" "Laaa wai kinji haushi ne? Tambayan raayina fa kikayi kuma na baki amsa...oh make nah calm downn o" "Excuse me?" Kwatseta Yusrah tayi cikin bala'i nan da nan ta saka ma fuskarta salon tijara "Dallah yi mun
Table of Contents