Chapter 2
Chapter 2
"Ohhhh ban hadu da wannan me sunan ba" "Ayyah sha'aninsu na manyan mutane qila ta yuwu hidima sun masa yawa....bari in hau sama ,ina jin barci kinsan ina on steroid drugs din kamar sedatives ne suna sani barci sosai" Yunqurawa tayi da zummar tashi kawai wayarta ya fara ɓurari. "Mr. AA" Taga yana yawo akan screen ɗin ta,dan washe fuska tayi,ta dauka da sauri "Big man big problem🤗(kirarin da Hajiya Juwairiyya take masa ke nan duk in sun hadu ko suna waya)....kaga ynz nan muke magana da auta take cemun bata ganka ba nace wani uzurin ne ya rikeka" "What???????? Innalillahi wainnailair rajiun " Zumbur Yusrah ta dago daga kwanciyar da tayi tana kallon mamanta "Momy is evrything ok?" Banza tayi mata tana cigaba da wayarta "My lord...Ba shekaranjiya kace ta biyo ka ba? Accident? Ya Allah gani nan zuwa" Ta kashe wayar ta haure saman dakinta da gudu ,dukda yusra nata tambayarta lafiya? Lafiya bata saurare ta ba taje ta dauko car key da dogon hijabi fari tar me bakin leshi irin na matan Alhazan nan ta fice da sauri tana qwalla ma driver dinta kira . Daga maitama gudu sosai yayi ya shata shataletalen Asokoro ya dangana da gidan Major Adeel inda ta sameshi shaqe da dan adam tamkar ba awanni hudu baya akayi rasuwar ba .Don daidai da gawar matar nashi ma ba'a kawo ba daga asibitin. Oum Aphnan 09065990265 [6/14, 11:42 AM] Chuchu👻: Page 12 Rasuwar matar Adeel ,ya gigita duk wani makusantarsu kama da en uwa da abokan arziki ,saidai dukda haka Adeel yayi namijin jarumtar da ba wanda ya taɓa tunanin zaiyi ,ko sau daya bai kwalla ba ,saidai shi yasan kurman kuka yake mai cin zuciya wanda gwara ma ya dinga rusa ihu in yaso a wuce dashi psychiatric .saidai saɓanin hakan shine mai ba wasu hakuri ina yaga suna zubda hawayen rashinta. **** Saida Hajiya Juwairiyya ta tabbatar an kau da gawar da ita sannan ta kira gida tace asa masu aiki su dafo abinci na sadaka sai driver ya taho da Yusrah ta masu gaisuwa su taho gida tare. Yusrah taso taqi zuwa sbd maganar Allah yau ta fara shiga office and ta gaji sosai .amma jin mamanta not in the mood of Nonsense yasa ta amsa mata . Dab da magriba komai ya kammala lafiyayyen white rice and stew cikin manya manyan kulolin biki da kaji daban a wasu warmers din dabam,suka zuba a back seat suka tafi gidan Major Adeel. Simple shiga ne a jikin Yusrah of just Black abaya ,sai qaramin earpod a kunnenta sai wayarta shikenan ta bisu suka tafi . Wow !! A bunda Yusrah ta fada a sarari kenan ,tabbas tasan kudi kuma ita girman kudi ne kuma rainon yawon qasashen tsakanin Ingila da Saudi amma tabbas gidan Major Adeel ya tafi da tunanin ta . "Subhanallh see how people lavishing things in dollars " she exclaimed! A sarari Yanda kuwa taga tsaron gidan saida yaso baya tsoro sojoji ne daddanke ,dukda tsaron ta karu ne sakamakon rasuwar da akayi baqi manyan mutane sun cika . Kanta a qasa ta shiga gidan saboda batta son ma yawan gaisuwa , don haka tunda ta shiga idonta na kan wayarta har suka isa inda Hajiya Juwairiyya take .suka diddirke abincin sadaka masu aikin suka koma mota suka barsu a nan itakuma Hajiya Juwairiyya bayan tai handing abincin ga makusantar Major ta kirasa a waya dinta shaida masa zasu wuce kuma ta sake masa taaziyya. "Hajiya ina cikin gidan bari inzo " abinda ya bata amsa dashi kenan ya kashe wayar. Aiko of just 8 to 10 minutes sai gashi yazo . Sam bai lura da yusra dake tsaye ba itama bata san dashi ba ,infact bata san ma gidan waye tazo ba ko waye ya rasu ba. "Ranka ya dade take her plz ,Allah yasa can ya fiye mata nan ,kayi hakuri kaji...mu zamu wuce dare yayi" Duk wanann maganganun da Hajiya take masa kawai gyada mata kai yake sam baya jin dadin magana . Juyawa tayi ta kalli direction din yusra da take ta shafa waya "Ga yarinya ta Yusrah zata maka gaisuwa " Lokaci daya suka dago gamida kallon juna . Wani irin balain shock ne ya kamata lokaci guda. Shikuwa wani irin murmushi yayi na iya fatan baki . "Sannu ko?" Ya miqa mata hannu don su gaisa irin tasu ta en boko ya mata dabiansu na wainda ilimin addini bai wadace su ba. Ta kasa bashi amsa saboda idonta da suka ciko da qwalla sai miqa masa hannu da tayi don suyi handshake ya kuwa riqe gammm yana jinjina mata🤝 Itakuwa ba radadin dugin damqe mata hannu ya dameta ba yatankacin tunanin.....kennan matar nan da ta kira a waya da gaske ta mutu? Qirrr ta masa da ido ba uhm ba uhm uhm "Yarinyar ki kyakyawa Hajiya kuna kama sosai " ya fada ba tare da nuna wani damuwa ba,amma still hannunsa rimtse da hannunta yana dandana mata azaba Hajiya murmusawa tayi ba tare da tace komaiba ,a ranta tana cewa namiji hoooo ana gaisuwar matarka amma har ka hango wata! Bakin yusra rawa ya shigayi saboda azaba qiris ya rage ta fasa ihu "I'm sorry For your lost,Allah ya jikan matarka ,Allah yasa ta huta" Qirrr ya kafeta da ido ba tare da yace Amin ba ko kuma ya cika hannun ta da ya rike kam. Cikin rawar murya mai cike da tashin hankali tace "excuse me Please zan tafi " A nutse ya saɓule hannunsa a hannunta aikuwa da sauri tayi hanyar qofa "momy ina jiranki a waje" ta fada a kasalance ta rasa ma meke damunta. Kallon Hajiya Juwairiyyan yayi "lafiyanta kalau kuwa?" "Ina jin ta rude ne kasan mutuwa ,bare su yara ,maybe tausayinka taji" Jinjina kai yayi "Nagode Hajiya Allah ya bada lada yabar zumunci" "Tom amin sai mun dawo goben" Oum Aphnan 09065990265 [6/14, 5:12 PM] Chuchu👻: Next monday Kamar ko yaushe a qasaitance ta shigo cikin kamfanin guard dinta na take mata baya riqe da jaka,haka suka shiga reception din ,tun daga qofa take bada umurni "Young lady this is not an office code plz karki sake zuwa muna da kayan nan...ke kuma my seceretary ,meeting nawa nike dashi yau? " Cike da girmamawa da shayi tace "uku ne ma'am" "Ok ina so ayi mun fixing wanda zanyi da Alhj munnir ya zama around 2 haka so give him a call let him be informed " "Yes ma'am" Cikin yauqi da tafiyar en gayu ta dangana zuwa wajen office dinta ,tana yarfe hannu tana wannan kalle kallen tana nemo abun magana da ido. Tafi taji a bayansu ,wanda ya sata waigawa da sauri. "Attention everyone!!!! Duk wani wanda yake aiki ya dakata ,a fice daga wannan ma'aikatan an rufe shi...in kuma ba haka ba!...." Da sauri Yusrah ta kwatse ta . "In kuma ba haka ba,sai yaya...? Excuse me Madam waye ke ma tukun?Kinsan kuwa Ni wacece a gavanki kike mun magana?" Kafin matar ta bata amsa aka turo kofa Major Adeel ne cikin shigar sa na cikakken soja mai tarin mukammai bayansa sojojine hudu suna take masa baya "Ita din ba kowa nace face Sabuwar Chief executive Director dina na wannan kamfanin..." Dukda ganinsa ya
Table of Contents