Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 7

Chapter 7

Namijin Zaki Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

yaji wuya yayi surrender " Cikin mamaki da qanqance ido yace "ke wai kin manta nan gidana ne?" "Ehen Ni kuma kace bamu da gida halan a bila ka tsinto Ni?" Cigaba da haurowa yayi cikin fusata ,ba abinda ya Qosa irin yaji ya damqi wuyarta Ai tana ganin hakan ta kinkimi botikin ruwa daya daga cikin wanda ta jere a wajen,kafin ya ankara ta sheko masa tun daga saman maɗigan kansa . Gantsarewa yayi ya bude murya yana kwarmato ya sakko qasan da sauri saboda kar tsantsin ruwan ya kadashi daga interlocks din da suke shimfida a wajen masu tsananin tsantsi kamar tiles. "Ni kike watso ma ruwa? Ni kike jiqawa?" "Badai You want to disturb my sleep ba? Badai nace ka koma sai na tashi ka dawo ba ,to wallahi in ka sake attempting haurowa i will sprinkle pepper 🌶️ a cikin ruwan inna hautsina ruwan da garin borkono na sheko maka zaka san dalilin da ake kirana small pepper 🌶️" "Yusrah kin shiga uku,Ni dai ko?" "Weeeeeh kaji tsoro wwweeeeh amasa a tule hauro mana ko tsoro na kake ji?" "Humm wallahi yusra You must pay For this wannan abun shine qarshen ki mu zuba " ya wuce da sauri yayi hanyar parking lots don barin gidan. Tale qafa tayi tana masa tafiyan en iska tana karkada masa medium nyash dinta ,girgiza kai yayi cikin malolon baqin ciki ya shige motan yana doka ma duk yaransa tsawa da gudu driver din yazo ya shiga don driving dinsa to the hotel. Oum Aphnan 09065990265 [6/26, 7:59 PM] Chuchu👻: Sai dare ta bude qofar wajen 11 ya dawo gidan bai cema kowa komai ba ya wuce part dinsa ya rufe kansa. *** Washekari Da yangarta ta fito daga bathroom tasha wanka tana tsane gashin kanta da qaramin towel ta tsaya a gaban mirror ta bude roban chewing gum mai qamshin vanilla ta saka a baki tana taunawa a hankali ta isa gaban closet dinta ta bude da nufin ta dauki kayan da zata saka Ya Salam! Wayam ta gani kamar an share. A tsorace ta isa gaban dayan ta bude shima wayam haka ta biya duk ukun babu tsinke me sunan kayanta sai wani madaidaicin akwati a qasan closet din ,cikin mutuwar jiki ta tsuguna ta bude akwatin abayoyine danke sunfi kala ashirin .Ai bata san sanda ta daura hannu aka ta kwarma ihu ba tayi waje karce ta fice da gudu tana kwarara masa kira "Adeel ?...Adeel??where is that devil in a man...ADEEL??" Tun daga saman bene take kwarara masa kira da qyar ta laluboshi a can garden din gidan yana zaune kan kujera yana karanta jarida kan table din gabansa tataccen fruits ne yana sipping a hankali ,kayan da yake sanye dashi na exercise ne wannan zai tabbatar maka da motsa jiki ya gama . Duk ihun kiransa da takeyi baisa ya motsa ba Sa da tazo gabansa ta rike kwankwaso "Adeel ban ga kayan sakawa na ba ,suna ina kenan?" Cikin yamutsa fuska na wanda baisan maganar da akeyi ba yace "to me yasa kike tambaya na" "Saboda daga Ni sai kaine a cikin gidan" "Ok jeki gym house ki duba " Dago kai tayi tana kallonsa "Rainin wayo ko me? Me zai kai suturuna wajen gym ?" "Ina ganin Zaifi maki dadi kije ki duba fiye da ki tsare Ni da tambayoyinki maras answer " Batabi ta kansa ba ta ruga da gudu hanyar wajen motsa jikin gidan saidai tun kafin ta qarasa ta soma perceiving qaurin kaya da suke cin wuta dararo idanuwarta tayi duk waje ta fasa ihu . A gigice ta dawo wajen sa tana aiko masa da zagi "Mugu Azzalumi kana ina ....maqetaci ina ruwanka dani wai me nayi maka ne akan me zaka tsane Ni ,ina ruwanka da kaya na ha'ahhh? Kawai gwara ka kashe Ni ka kashe Ni ka huta Adeel " Tana magana ne jikinsa na rawa hawaye na tsiyaya mata a fuska. Cikin rashin damuwa ya dago tamkar baiji duk abunda take cewa ba "Aah wai kuka kikeyi?Gani fa nayi wannan kayan da kike sakawa sun cika yin tsirara tsirara,wannan ya baki daman juya mun jikinki anyhow a gaban yaran aiki na ,soooo naga ya kamata in qonasu ,tun da dai Matana tana da decent clothes sai ki cigaba da sa kayanta,kinga in na ganki a cikin kayanta zai ringa tuna mun da ita...ko an fada maki zaki shigo mata gidane kina mata shigan fitsara kamar wata model bayan kin kashe ta?" "Oh🤨🤨🤔Kana nufin ka qona mun rankatakaf designers din kayana masu arnan kudi da tsada ? Kana nufin ka kona mun unique kayana da ba'a samun irinsu ko a qasashen waje sai mugun sa'a? DUK SABODA IN SA KAYAN MATACCIYAR MATARKA???" cikin murmushin qeta ya amsa ta da "Eh kuwan" Dafe kai tayi cikin rashin madafa "Oh my goodness wai ma taya na hadu da wannan mutumin ne mai ciwon Qwaqwalwa ma tukunna ,ya Salam!!! Ni zansa kayan gawa?....humm kasan menene? Wallahi wallahi na tsane ka!!!" Ta juya bakan bakan zata wuce ciki . Dariya ya kece dashi,wanda ya sata dakatawa ta waigo tana kallonsa "hhh wannan qumbunan roban da kike sakawa da wannan parking din gashin kanki da kikeyi kamar er bebin roba dama ina so in maki warning tabbas ki daina dole ki zama er gargajiya irin matata ,shigar riga da zani ki daure kanki tamau da kallabi gashi daya bana son ya leko waje ,ko atamfa ko riga da zani sune kadai kayanki a gidan nan kuma kar in sake ganin kanki ba dan kwali " Dariya ta fashe dashi "oh really ? Baka da lafiya bai kamata ina biye maka ba kaje ka nemi consultant na mahaukata" "Oh yes! And na manta ban fada maki ba duk wa'innan takalmar naki na rashin da'a duk na qonasu ..." Waro ido tayi ta nuna shi da yatsa hawaye na shararo mata a kunci "Ka qona mun takalma ,Adeel kasan yaya na same su kuwa?" Oh yes ! And in addition,Duk account ɗinki na bankuna na rufe su ,na lura duk su suke saki zama almubazzara ki ta facaka da kudi so na rufe" ita ko jin surutansa ma bata yi kawai tunanin tsadaddun takalmarta takeyi ,idanta nakan bakinsa har saida yayi shiru tace "Adeel ka qona mun takalma? Worth more than 33m dollars?😭 Jinjina mata kai yayi yana murmushi . "Adeel ka qona mun takalmana qirar malaysian,Arabian,Indian ,europian duk ka qone su? Duk na rasa su kake nufi🙆‍♀️😭😭😭? Dafe kai yayi da sauri alamun ya tuno wani abu Da sauri ya daga mata hannu "kinga sorry kar ki mantar dani wannan,dan saurara in fada maki........Idan har kinaso ki cigaba da cin abinci a cikin gidan nan topah dole kiyi girki,matata ta iya girki musamman take dakamun yajin citta yajin gauta yajin daddawa duk wa'innan traditional abubuwan dole ki koya yin mun su... otherwise duk businesses din mu da companoninmu Are nollified!!!!! Dake da uwarki zakuyi Bara a kwalta" yana fadin haka ya mike a hankali ya dauki glass cup din tataccen ƴaƴan itacensa ya kurba Harraqo masa tayi da fitina da sauri ya dakatar da ita ta hanyar cewa "kamar na manta ban fadi wani abu ba...oh yawwa Dabi'unki na banza dole zan sauya

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16