Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 12

Chapter 12

Namijin Zaki Book 1 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

mata a dare ɗayan nan taji ya cure mata a qirji a haka barci ɓarawo ya sulale ta itama. **** 5.15am Yusrah ta riga Adeel farkawa daga barci saboda duk iskancin Yusrah sangarta bai hanata sallah akan lokaci ,farkawa tayi ta janye jikinta a hankali a jikinsa sosai Adeel yaji dan nauyin dake kusa da qirjinsa ya ragu wannan ya kaima hormone dinsa signal ya fara mormotsa Idanuwarsa yana son buɗesu. Yusrah rafka tagumi tayi ta ɗan kishingida a gefensa tana qare masa kallo ,ashe dai Adeel mugun kyakyawa ne ? Me yasa na kasa ganin hakan tuntuni ? Ga quruciya ga Naira da daloli ga motoci ga gidaje da jiragen sama ,ga jarunta irin na manyan sojoji uwa uba ga hakuri da jure iskanci da haukan ƴa mace ....kallon kowani gaba na jikinsa take musamman kan nono sa da suka ɗan kumkumburo kamar irin na matasan qwailaye din nan zasu fara nono kafe su tayi da ido tayi sosai tana ɗan murmusawa ,wanda ita kanta batasan dalilin murmushin nata ba. Waras Adeel ya sauke idanunsa akan fuskar yusra dake qumshe da murmushi ilahirin hankalinta na kan qirjinsa. Gigif ya motsa ya saka hannunsa cikin duvet din da ta rufa masa a saman jikinsa zuwa qugu ,da sauri yakai hannunsa kan kayan marmarinsa😊daga shi sai dan kamfai ya jisa yanda dai zuby ta tafi ta barsa. "Me kike mun a daki?" Ya tambaye ta a firgice Yusrah kam ko a jikinta sai ma qara yalwatar murmushinta da tayi zuwa qaramin dariya maras sauti "Good morning" Ko kallonta baiyi ba ya sake dan hangade duvet din yana qare ma kansa kallo "Ya na ganni tsirara 🥹"? "Circumstance" "Baki bani amsar tambaya ta ba ,ina kayana nace?!" "While laifine don ka ganka tsirara bayan kana tare da matarka?" Ta bashi amsa tana karkada masa ido cikin gari da kisisina. "Wait wait ,karkice mun kin mun fyade"? Murmushi tayi mai tsananin qayatarwa "Tabbas munyi komai da komai....ahhhh dama haka kake? You Are a bad guy... Wallahi ka iya tattalin mace a gado ,hummmmm ahhhhh Allah nagode maka da na samu ingarman miji kamar ka..." Ta qare maganar ta tana kai hannunta gefen hannunsa tana shafa masa daga kafadunsa zuwa qasa . Qif qif da ido yayi yana kallonta tana wani irin karairaya tana lashe leɓenta na qasa tana jan numfashi ciki ciki. "Ke ke kice mun wasa kike mun,wannan ma ai ba'a ne!" "Akan me zan maka wasa ? Da gaske ka iya 😂" ta fashe da dariya lokaci daya kuma ta gintse fuska ta dirka daga kan gadon ta wuce tana jujjuya masa en madaidaitan mazauna ta da suka saje da ɗan slim jikinta ,ta bude qofa ta fice a dakin ta barshi a nan yana bin bayanta da kallo yanajin kamar ya cafko qugunta mai dauke da er farar short din nan yayi wasa dasu .saidai inaaa qwalelensa. "Auccchhhh " ya kaima katifar da yake kai naushi yana ayyana abubuwa a ransa. Oum Aphnan 09065990265 Littafin kudine dai ,You can get yours by sending your payment via this account details 9065990265 Opay Mohammed Hassana Ko 7782217014 Fcmb Mohammed Hassana [7/6, 7:25 PM] Chuchu👻: Yusrah tana zuwa dakinta wanka tayi tai brush ta dauro Alwala ,ta shimfida praying mat din ta ta gabatar da sallan farilla ,tadan tsaya tayi addu'ointa da ta saba ,saidai haka nan ta tsinkayi leɓenta na masu addu'an zaman lafiya ita da mijinta ,tare da fatan sanya ma zuciyarta ruwan sanyi ta daina masa rashin kunya kuma tayi masa biyayya gwargwadon Iyawanta. Cikin hawaye ta ninke darduman ta wuce kicin ta soma hada masu break fast . Doya mai yawa ta fere tasa a wuta tana simmering dinshi in a low flame ta qara pintch of salt da sugar For taste ,kana ta dakko kayan miya tumatur ,red pepper da bell pepper ta gyarasu ta zuba a blender ta niqasu ta bude fridge ta dauko kankana wanda bai nuna sosai ba da kwashe ciki ta fidda seeds din ta zubar ta nike kankanan ta cakuda da kayan miyan ta zuba a cikin tukunya ta zuba tafasasshen naman rago da left over din soyayyen kazan da take dashi. Kafin ta gama haɗa wannan stew din doyanta yayi laushi ta tsane ta soya shi da isashen kwai ,ta zuba a mazubi mai kyau ta rufe da foil ppr ,ta dawo ta sa wani tukunyar ta daura dahuwar white rice da yarfin peas a ciki . Cikin qanqanin lokaci ta gama komai ta gyara ta haɗa masa lafiyayyen shayi irin na larabawa harda su cloves da na'a na'a tasa a qaton Flask din gida wasu kuma duk ta diba ta zuzzuba a jakan abinci . 7.15am komai nata ya daidaita ta dauko kayan abincin ta wuce dashi zuwa wajen compound dinsu ta damqa ma driver dinsa tace ya saka masa a mota . Sauran tea da fried yam din ta dauko zuwa dinning ta ajiye condensed milk dinta da evaporated milk sai milo da raguwar cake dinta na fridge ta jere a wajen ta kunna ma dinning din turare mai sanyin kamshi ta fito falon tana mopping karafaren wargajejen falon . A nutse ta gama shima tabi labilen tana turare su da kamshi zuwa kujerun ta dawo da qaramin towel din hannunta tana karkade kayan kallonta zuwa manyan aljifan maajiyar TVn .all of a sudden ta zaro wasu folders wanda taga kamar da safe ya fita dasu ,debosu tayi da nufin ta kai masa daki .sai washarrrr suka zube a qasa "Subhanallh" abunda ta furta kenan ta duka tana tattarewa "Ya salam!!" Hoton Nutsatsiyar mace ta gani ta nade jikinta cikin abaya mai ruwan jinin kare ,fuskarta fal fara'a sai qyalqyali take cikin gwala-gwalai . Yusra ji tayi kamar an sassara mata gwuiwa dakyar taja jiki zuwa gaban kujeranta ta zauna yaraf hannunta na kakkarwa riqe da hoton matar Adeel Kafeta da ido tayi bakinta na rawa na wanda kuka yake son cin qarfinsa "Kiyi haquri ki yafe mun...ban da nufin sanadiyyar barinki duniya balle har in maye gurbin gidanki ,ke nutsattsiyar macece da duk wani namiji zai fatan samunki matsayin matar sa ,daga sanda naji adduoinki akan mijinki naji kin sauya mun rayuwa ,naji kin burgeni naji sonki yana ratsa bargon jikina, naji ina ma kina raye inje in sameki mu zama qawaye ko kya bani shawarar zaman duniya ?!!! Amma kuma a yanzu da na ganki gani sai naji na tafka kuskuren da bazan taba gyara shi ba ,dole ne in amsa hukunci a wajen mijinki ,banga azaban komai ba ,kuma tabbas na cancanci hukuncin da ya fi hakan ma ,amma plz ki yafe Ni kuma inaso ki sani mijinki yana sonki kuma nasan bazai taɓa qaunata ba har abadan...amma nayi maki alkawari zan cigaba da kula maki dashi har iyakan numfashi na na qarshe wannan fansan ranki ne da soyayyar ku ...😭😭😭" Kasa cigaba da maganar tayi saboda yanda kukanta yaci qarfinta wani irin kuka mai shesheqa da kururuwa takeyi kamar wacce ta rasa komai nata na rayuwa. Adeel dake tsaye kamar drawing yana jin duk abinda Yusrah ke cewa ,yana ganin zata dago yayi gaggawar ja da baya da baya har ya isa qofa ya bude a hankali ya fice zuwa office. Oum Aphnan [7/6, 8:26 PM]

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16