Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 5

Chapter 5

Namijin Zaki Book 1 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

nazo ba haka yake ba wannan gida mai suffar jirgi fa ,ga wasu gangama gangaman gate kamar na masarautun indiya ,ga wasu sojoji sai kace su zasu hana dan adam ya mutu go tulin motoci sunkai ashirin wanda itadai in ba qarya tayi ba wanda ta taba ganin irinsu basu wuce biyar ba ,ga mashin nan irin na tseren gudu sunkai biyar kakkafe a rumfunarsu. Tacan gefen gidan wajene akayi fensing dinsa aka malale wajen da adon grass carpet da er madaidaiciyar jirginsa helicopter a kafe. Dafe baki tayi ,wai shin Ni kuwa wani irin kudi mutumin nan yake dashi?? Duk wannan abubuwan a abinda bai fi second goma ba ta qare na komai kallo .Sarai tana jin yanda danginta suka gigice da kudin Major Adeel da yanda suke zuzuta motocin daukan amarya duk sababbine daldal a leda kuma daidai da tint din motar ruwan toka ne wanda sam babu mai irin tint din sai gidan Major . Kuma yanda aka shiga da motocin aka ajiye su haka duk suka fito kowacce aka danqa mata key din motar Ba wasu dai zafafan motoci bane masu tsada Corolla S ce amma fa ya tada hankalin danginta .kowa sai fatan Alheri yake da fatan kar ta bawa mata dansu kunya. Oum Aphnan [6/15, 7:15 PM] Chuchu👻: Da kansa ya bude mata kofar shiga tangamemen living room din gidan,Yusrah kam cike da yauqi da daga kai take tafiya har ta shiga dakin da yafi dacewa da a kirashi Aljannah duniya. "Barka da zuwa gidan Adeel" Kallonsa tayi irin kallon Nan mai cike da harara. "A cikin wannan mansion din akwai dakunan barci guda sha biyu,Manyan dakuna guda bakwai,wajen hutawa guda uku garden biyu,awimming pool baban daya kananu biyu ,dinning room uku ,sashen baqi da boys qtrs......" Tunda yake magana ta qame qam nade da hannu a qirji tana jin duk wasu bayanan shi har saida yakai qarshe kana ta daura da tambaye cike da gatsali da izgilanci "...and so..?" "Yes so,akwai wasu dokoki da zan shimfida wanda binsu diqin diqin farilla ne...idan kuma aka qi bi za'a fuskanci tara mai girma" "May I?" Ta tambaye shi sannunsu in single words "Kamar yanda dai kika ga gidan nan bai kama da gidan Tsoho da tsohuwa ba ,to la shakka duk abunda kika ɓata sai kin biya" "Ban fahimta ba🤨saboda ka kawo Ni wannan kejin da kake kiransa gidane zaka ishemu da gadara? Can U listen to ur self ? This is silly jokes" "To shikenan zaki fahimci ba'a iya ganin ki....Umurni na farko shine zaki ringa wanke gidan nan ciki da bai duk sati ,i mean har bangon gidan nan sai kin wanke ai dai kina ganin fentin leda leda ne ba laifi bane in an wanke....Na biyu wanke wanke farilla ne safe da yamma da duk sanda akayi mun kalar abincin da na bushi iskan ci......oh biyoni muje in nuna maki wajen wanki" cikin taqama ya fara takawa tas tas Wani dariya ta bushe dashi gami da jan tsaki. "Mtsewwww kana shirme ,Ni in bazaka iya nuna min dakina ba Bara in je in nemeshi da kaina " ta wuce fuuuuuu ta barshi anan wajen . Their first night a haka ya gantale.don tuni tai ma kanta mazauni a dakin qasa kuma ta mirza makulli tayi wanka ta miqe a gado. Oum Aphnan [6/15, 7:41 PM] Chuchu👻: Washegari Ya kama monday ,qarfe takwas Yusrah ta fito ta fesa wanka cikin wasu suit riga da wando baqaqe sai rigar ciki royal pink ,ta saka takalmi da jaka masu musulman tsada ,ta maqale agogon ta na diamond da dan kunnen diamond ta fito fuskarta fayau sai sheqin man baki yake ta tufke tulin gashin kanta ta baya ta ɗan yano siririn mayafinta mai kama da maka wuya saboda ba abinda ya rufe rabin gaban gashinta a bude kazalika iska na ɗan ɗagawa za'a hango tulin gashinta ,wannan mayafi bacin tsawo da baida banbanci da handkerchf. Cikin cat walking tazo ta wuce shi a falon yana zaune yana kallon CNN taje ta murde qofa ta fice ta isa asalin main door din da zai sadaka da farfajiyar gidan shima ta murda zata bude saidai kuma garam ta jishi a garqame ,ta murza handle din ta mirza amma fa kan kam ba ya ko motsi . A yatsine ta dawo gabansa ta tsaya ,shikam ya dage kansa kan kujeran ya lumshe ido tamkar baisan da ruwan tsuruwanta ba dukda lafiyayyen qamshin turaren ta da ya masa maraba "Zan tafi office a bani makullin kofa" Ba tare da ya dago ko ya bude ido ba yace "....Doka ta ta biyu kuma...,Matata dole ta zama sit at home house wife ,cikakkiyar matan gida nike nufi" "Ni?😳Ni yusra carrer lady kake dangantawa da matan gida? Ka manta daga family din da ka dauko nine ? Kaga nayi maka kama da matan gida ?" "Halastaccen aure nayi bisa sadaki don haka a aure babu sharadin fita aiki ,tabbas kamfanonin da duk wasu kadarori yanzu naku ne amma ke?! Ke?! Bake zaki dandani dadinsu ba...ki fara qirga kanki a matsayin house wife not a carier wife" "Humm Adeel You Are not normal ? Me kake so inyi hannn my friend ban key in fita jhorrrr " ta qare maganar cikin tsawa tsawa da hassala "Ki wuce sama ko sauya kayan jikinki na tanazan maki riga da zani da dan kwali ki sauya kayan jikinki dasuka fi suffan taki da bayahudiya .ki saka kayan da na tanajar maki irin namu na Hausa Fulani .in kin gama tassss ina jiranki da tuwon dawa miyar farar kuɓewa ɗanya da stew din kayan ciki da ganda. " Riqe haɓa tayi tana kallonsa🤔mamaki zatayi ko mene ma oho "Yauwa a matsayina na bafullatani ki tabbatar ki soya mun isasshen man shanu yaji albasa ki taho mun dashi" "Kai wai ban gane ba ,dani kake yi?" Sai sannan ya dago yana kallonta ya dan kai hannu ya dauki cup din drink ya kurba "Uhm uhm ba dake nakeyi ba da inuwar ki nakeyi" yana kaiwa nan ya yunkura a hankali ya mike yana gyara zaman guntun wandon sa na sojoji .hannunsa rike da glass cup din drink dinsa. Itadai tana tsaye qiqam kamar drawing har yazo dab inda take kana yayi magana a hankali daidai kusa da kunnenta "Ina jiranki a sama da abinci na and karki manta da soyo mun wadataccen man shanu...." Mamaki ne yasa ta hangame baki har ya wuce yau ya kasa bashi amsa . Sai da tayi kamar second biyar kana tace "Ni Yusrah? Hummm wannan mutumin bai Sanni ba" Oum Aphnan [6/15, 7:59 PM] Chuchu👻: Bayan awanni uku Bankado kofar dakin taji anyi wanda ya sata mikewa akan gado a firgice gamida dafe qirji "wash Allah na" "Meye haka? Ke Ni fa bana jurar jira bazai yiwu ba kuma a matsayina na soja bana wasa da cikina,me kike yi anan ? Ina abinci na?" "Wai waye zai ma girkin?" "Ke ! Ke nake nufi ai siyanki nayi da sunanan kudi masu yawa ,don haka dole ki mun bauta a gidana aikinki shine ki kula da Ni ,aikin ki shine ki mun girki ,aikinki a gidan nan shine ki mun wanki,sannan ki bani lafiyayyen sex a duk sanda na buqace ki a gado

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16