Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 13

Chapter 13

Namijin Zaki Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

Chuchu👻: Yusrah zama da Major Adeel ta fahimci mutum ne mai son gida ,sannan yana son yaci abinci a gida musamman na gargajiya ,kuma ta karanci duk inda 6pm yayi to yana hanyar gida .don haka tun 4.30 ta tashi ta sake gyara gidan ta sauya ma gadajen gidan sabbin zanin gado ta wuce kicin dinta na second floor ta samu dogon stool ta zauna ta shiga youtube ta yi searching vegetable couscous sbd tasan dai bazata iya masa dambu ba . Tana kallo tana girkin ta har ta haɗa kyakkyawar couscous yaji hanta da veges ta yi masa kunun aya mai dadi ta maida a fridge ta haɗa masa shayi mai kyau daje ta jeresu a dinning ta saka turare mai fidda ruwa. Tana jin qarar shigowar motocin sa ta haye saman dakinta da sauri sam bata son su hada ido dashi kunyarsa yanzu take ji . Wani sanyin niimtaccen dadi yake ziyartar kofofin hancinsa tunda ya shiga gidan ,cike da zaquwa ya je yayi wanka ya wuce dinning dukda Yusrah ba gwana bace a girki amma iya dan training din muguntar da zuby ta bata da dan zama da qawaye yasa ta ɗan koya ba tare da wahala ba ,sannan wani abun jin dadi abincin yayi dadi tamkar qwararriya,yaji dadin abincin da takai masa office sannan yaji dadin ganin na dinning na jiransa . Saida yaci sosai shi kansa ya manta when last ya nutsu yaci abinci haka in baiyi qarya ba tun kafin matarsa ta rasu . A daki kuwa yusra bayan tayi wankanta ta sauya zuwa kayan barci qarfe tara ta feshe jikinta da turare ta haye kan gado tana cigaba da kallon yanda ake tuwon samo ta youtube. Adeel knock daya yayi bai jira izininta ba ya tura kai cikin dakin . "Hi" Murmushi tayi masa mai fadi ta kife fuskar wayanta akan gadon saboda kar yaga me take gani "Me kike kallo?" "Ina koyon yanda ake tuwon semo ne,gobe zan ma shi shine nake ta bita" "Hhh shine ya saki nishadi har hakan?" Rausayar da qwarorin idonta tayi ,ta na ɗan sosa kai cikin jin kunya. "Ohh kalan naki salon yaudarar kenan? Shiyasa kika kashe mun mata? Saboda kizo ki zambaceni? Kin kashe ta ke kuma don ki samu ki maye gurbin ta!" Cikin mamaki ta nuna kanta da yatsa "Wai Ni?" "Aah bake ba Ni" "Haba Adeel ya kamata zuwa yanzu ka dauki qaddara ko matarka ta kwanta lafiya a kabarin ta kayi hakuri kaji duk kuskurene kuma an aikata ba kuma zai gyaru ba" "Baki isa ba ,yanda banyi farinciki ba haka kema" Cikin sarewa ta mike tsaye "Haba Adeel ya kake so inyi da rayuwata ne...in nayi masifa kace nayi and now i am trying to fix it..." "Fix what? Shedaniya makira algunguma?!" Dafe kai tayi cikin ɓacin rai kawai a harzuqe ta dago "Adeel kasan menene kawai ka kashe Ni! Aidai kana da bindiga ko? Ka dauki matakin da ya dace ka kashe Ni ko ka fanshe haushin na kashe maka mata,meye amfanin ka barni a raye kana ganin ajalin matarka?! Kashe Ni kawai ka huta zaka iya kuma ba wanda zai tuhumeka doka ta baka dama" "Ke Ni zaki isheni da barazana? In na kasheki kina nufin kinci banza kenan? To baki isa ba sai kin fada mun me yasa kika kashe mun mata" "Kai kanaji ko? Na gaji kawai na gaji sake Ni inyi gaba na yarda talaucin ya kashe mu Allah da ya bamu a da in ka qwace in da rabonmu zai qara mana wani...don haka sakeni inyi gaba " "Bazan sake ki din ba anan zaki mutu" "Kai mahaukaci ne🤧" ta juya bagazan² zata fice .da sauri ya bi bayanta "Waye mahaukacin?" "Nace kai!........" Daidai nan ta wangale kofa kuma a take ta hadiye miyan bakinta ganin wanda ke bakin qofar .yanda ta ɗauke wuta shima haka Adeel da ya biyo bayanta ya ɗauke wuta cikin mugun razana. Oum Aphnan 09065990265 [7/6, 9:57 PM] Chuchu👻: Dafe baki Yusrah tayi da sauri cikin trembled voice tace "momy!!!😳" A gigice Adeel yace "aaaaah manyan baqi mukayi haka...Barka da zuwa sannu da zuwa" Gabadaya Hajiya Juwairiyya shan jinin jikinta tayi don haka a kasalance tace "yauwa ya kuke" Kamo hannun yusra yayi yana murza mata en yatsu ita kuma sai murmushin yaqe take "wallahi muna lapiya" itakuma yusra ta tabbatar mata ta hanyar gyada kai "Sweery daukan mata kayanta mana mukai ciki" da sauri Yusrah take zata dauki cartoon din gaban momy .da sauri uwar ta dakatar da ita cikin mamaki ,yaushe yarinya na ta soma aikin qarfi har haka? Amma a zahiri sai cewa tayi "aah noo,ina masu aikinku naga kawai wulkawar uniform din sojoji nike gani ba er mace" "Aah momy😃Ba wani jan magana da tsayi bari in daukan maki muje daki kinji " cikin murmushi ta kinkimi cartoon din tayi gaba ,cikin sanyin gwuiwa tabi bayanta ,shikuwa sai washe baki yake yana ɓaɓatun sannu da zuwa. Tana wucewa ya kame baki ya gartsa ma yatsansa cizo "Me ya kawo matar nan cikin dare gidan surukanta ,kardai tace kwana zatayi kardai an kai mata tsegumi" Washegari Tun dare Adeel yasa aka masa ordern abun break fast a wajen near by restaurant da kansa ya jere masu a dinning ,ya zauna yayi tagumi yana jiran fitowar su .yusra ta fara fitowa da shigar bom short da er ɓingilar riga taso tayi girki amma ganin komai a jere cikin warmers na alfarma yasa tazo ta giftashi sai bulbula qamshi take ta isa gaban warmers en tana bubbudawa "uhmmm farfesun turkeyn H &J ne wannan...awwn i missed it" Harara ya banka mata da murya qasa qasa yace "mayya abunda kika iya kenan wai tsabagen bala'i har qamshin girkin kowani gidan abinci kin sani..." Yatsine ta masa gamida harara "har ma da ɗanɗano duk ma sani mtsew marason zaman lafiya kawai" "Kece dai fitinanna laluwa masifa" "Kai wallahi You cant overshadow me bar ganin momy tazo Ahaa" Magana suke qus qus amma masifa sukeyi kamar zasuci kansu ,a nutse momy ta iso mayen dinning din Da sauri dukkansu suka miqe . "Hello my beautiful angels" "Sannu momy an tashi lafiya ya baqunta" "Aaah Alhamdullh ,ku haka kuke break da wuri haka" "Yes momy kinsan yana zuwa office da wuri" "Yeah i see" Taka kujera ta zauna sai sannan suma duk suka zauna A nutse suka fara cin abinci amma sukam qirjinansu sai lugude yake "Ya ya kuma zaune lafiya dai ko?" "Aah wlh lfy qalau ,Yusrah kyakkyawar matata ga qwazo" Tattare giran sama da qasa tayi ta kasa tantance sambatun da yake "qwazo? A gidan auren? Boyi boyi kike?" "Kai momy Yaren sojoji ya maki ,plz mu sauya fira zuwa na nishadi mana momy" "Oh really? To yaya jaririn ku ? Yana lafiya? Wani asibiti kukayi registar na yin awon cikin...." Tuni cikin Yusra ya fita ruwa quuuuuu,wani cikin mijin ma da bata taba sani saba "Am...aiiii....ehhh nayi ɓari ne satin da ya gabata" "I see😏🤨" ta basu amsa tana cin abincin ta "Eh momy karfa ki damu sa far as muna son junanku bamu cire tsammani ba a shekara ɗaya ki ganmu da en uku" a tare su biyun suka fashe da dariya wanda dukkansu bai kai zuciya ba

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16