Chapter 14
Chapter 14
"Kun tabbata kuna zaune lafiya kuwa?" "Sosai ma" suka bata amsa kamar hadin baki. Kallon su tayi daya bayan daya "ok Ni har mutane sun kai mun mummunar labari amma bakomai zan ganinma idona ,as U saw me yesterday i had a plan to go to Canada but i lost my trip so sai nan da kwana biyu shiyasa nace Bara in zo in spending a gidan yarinyata nayi kewarta sosai dukda ita bata zuwa wajena ....ko bakuyi farinciki bane naga duk kun guntse fuska. "Kai kai farinciki mana ,momy ai nan gidan damu da abunda ke ciki duk ikon ki ne" "Ok tnk U my children nidai Bara inje in dawo kamar nayi mantuwa a ciki" Ta mike tsam ta fice ,tana bada baya yusra ta kalli hannunta da ya rike ta wani wancakali dashi "Dalla mu cikamu" "Dalla Ni karki isheni da pretending nasan kece nan kika kirata" "Kaidai ka kirata saboda na watsa maka ruwa na sattar maka da tayar mota and on and on..." "Mayu kawai a zo za'a kwashe mun dukiya" "Kaine dai maye qatoton ma" "Bari ta tafi zaki maimaita mun ne" Oum Aphnan 09065990265 [7/7, 7:22 PM] Chuchu👻: At Night Yusrah tana ji tana gani ta dauko pillow ta wuce dakin Adeel gudun kar momy ta saka mata ido ,saidai tana shiga dakin yayi zubut ya mike zaune. "Me ya kawo ki dakina kin wani rungumo pillow" Harara ta Banka masa "Ni fa tsiyata da kai takalan fada in bacin momy me zaisa inzo ince zan kwana a dakin ka? Da na zo?" "Shut up ur mouth ,duk yawan dakunan dake gidan nan bazaki iya zuwa ki laɓe a wani ba sai nawa to kuwa sai kin fita" "You know You Are just something else ,don Allah mubar fitinan nan saboda momy in ta tafi a cigaba" "Bazan bari ba kina jin tsoron ɓacin ran mamanki amma Ni kika dasa mun ɓacin rai For life? Kin cuce Ni Yusrah ,wai fada mun ke wata irin muguwa ce?" Tsaki taja kawai tayi kwana ta haure kan gadonsa "Zoki fita!" "Naqi din ba inda zani" Biyota yayi kan gadon suka fara kokawa yanason ya kinkimeta yayi waje da ita itakuma ta rirriqe zanin gadon.tana kururuwan ba inda zata . Cikin barci Hajiya Juwairiyya Sadiq take juyo ihun Yusrah sama sama kuma take jiyo Muryar Adeel yana ce mata ta fice ta bashi waje.zuruf ta zura takalmi da dogon hijabi ta nufi hanyar da take jiyo ihunsu da sauri. "Baka da tawakkali ,ka zaɓi kayi ta punishing dina bcuz of your late wife ,to na gaji wlh na gaji kuma fita bazan fita ba" "Zakuwa kiga bala'i ganin idonki" "Ya Salam Allah ya mana tsari dashi ...." Muryarta kawai sukaji a saman kansu ,tsit dukkansu sukayi kamar ruwa ta cinye su. "Baku kyauta ma kanku ba kuma kun tozarta niimar da Ubangiji yayi maka na lafiya da dukiya ,and above all kuna qoqarin ruguza rayuwar quruciyarku.....now yusrah jeki tattare kayanki ki taho mu tafi." "Momy kiyi hakuri inason in zauna" Wani irin tsawa ta daka mata wanda ya sata daukan rawan dari tunda take bata taɓa ganin tayi mata irin tsawan nan ba ,not only her harta Adeel saida hantar cikinsa ya kaɗa ,a iya saninsa da Hajiya Juwairiyya macece mai saukin hali da taushin hali,but why? "Nace wuce ki kwashe kayanki mu tafi and now!!! This minute!!!!!" Raɓawa tayi ta wuce tana zuwa bayan momyn ta tsaya tana hararansa da murguda masa baki ,kana ta bude kofar ta rufe gararam!! A nutse Hajiya Juwairiyya ta isa gabansa da sauri ya sunkuyar da kai saboda tsananin kunyar da ya rufe sa "First thing gobe da sassafe ,zan signing a jikin duk documents dinka ,kama daga companies ,estate da gidanmu ma da muke ciki ,amma kafin nan yau a daren nan zan tafi da ƴata..." Kafin yayi magana ta fice gamida dako qofar da qarfi. *** "Momy don Allah ki bari in cigaba da zama dashi ai bai taba duka na ba ,and beside bana son ya kwashe komai da muka mallaka momy mu dawo talaka" "Sai me in mun talauce su sauran talakan ba bayin Allah bane kuma Allah ma yafi son talaka mai tsoron Allah.a ranar lahira Allah yana cewa akwai mutanen da yake jin kunyar hada ido dasu na daya ,wanda Allah bai bashi haihuwa ba na biyu...." Katse ta yusra tayi da sauri cikin kuka "Shikenan momy kin fara mun waazin talauci a maimakon hiran juya Naira ya dawo dollar what the hell😭😭😭" "Ehh akan farinciki kine Yusrah bazan taba bari ki zauna da mutumin da yake zargin ki a kisan matarsa ba ,wallahi har abadan bazai soki ba,da kiyi rayuwar qunci a daula gwara kiyi rayuwar dadi a talauci....always remember ke kadai Allah ya bani kuma ke din marainiyace na rasa mahaifinki amma inna tunosa na tuna ya bani ke sai inji sanyi a raina ....yusra idan baqincikin da namiji ya haddasa maki bugun zuciya kika mutu kika bar duniyar nan bazan yafewa kaina ba ,don haka yusra ƴata kitattara kayanki mu tafi ,garinma duk zamu bari mu samu wani keɓantaccen qauye muyi rayuwar mu cikin farinciki" Jinjina mata kai yusra tayi cikin sharɓen hawaye ,bata taɓa sanin maraici masifa bane ba sai yau ,ya rab! "Momy ki yafe mun zan bi dukkan umurninki kuskure na aikata kuma inshaAllahu ya zame mini izina ashe fushi dokin nadama ne,ashe rashin hakuri babbar Misifa ne ashe gaggawar yanke hukunci ke kai mutum ga da na sani ,nikam naga nawa kalan qalubalen" Ta faɗa jikin mamanta tana shesheqar kuka mai taɓa zuciya. "Look You mean alot to me ,my yusrah zan iya sadaukar da komai nawa don farincikinki amma as U knw that kinyi kuskure ina rokonki kafin mu bar Abuja kije ki nemi gafaran Adeel ,maganar gaskiya kin cutar dashi" "Yes momy i will" *** Da duku ² momy taje office din su Adeel da kanta takai masa duk documents din komai da komai da wani er guntuwar wasiqa a envelope taba sakataren sa ta ajiye masa .ta bar yusra na hade kayan su .itakuma ta wuce cikin gari don suyi magana da qawarta inda zata samo masu gidan haya a irin unguwannin masu saukin qarfi na Abuja ta yanda zata fara business koda na waina da miya ne ko kosai da fanke . Oum Aphnan 09065990265 [7/7, 8:37 PM] Chuchu👻: Lastly Alhmdllh 🙏🏽🙏🏽 Yusrah rututu tayi a qasa tana bawa Adeel haquri fuskarta kace kace da hawaye ,Adeel da bai dade da gama karanta takardan momy ba,hasalima jikinsa a mace yake hannunsa riqe da takardan ,ji yayi duniya tana juya masa . "Ka yafe mun Adeel wallahi tun asali ba so da qauna yasa na shigo rayuwarka ba kazalika yanzu zan fice ba tare da na samu ko digon affection a kanka ba face ina tsananin nadamar abinda na aikata kuma ina rokonka ka yafe mun ko na samu in yi sabuwar rayuwa ta cikin aminci Adeel" Ji yayi kamar tana sake watsa masa wutan tausayinta a ransa ,sadda kai yayi yana jin wani irin baqin cikin saka ta kula da yayi For long ,yanda ta qanqame qafafunsa ji yake kamar tana qara masa wutan tausayinta ,a gaggawce ya fizge qafarsa tayi wani
Table of Contents