Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 10

Chapter 10

Namijin Zaki Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

Taji ta yanke ta da gigitaccen mari ,da sauri Yusrah ta dafe kunci ta fasa ihu ,Adeel kam da sauri ya rimtse ido ya toshe kunne yana dan murmushi . "Sai yaushe zaki koya dabian iya magana? Ehyeh?" Dago jajayen idonta tayi suka kalli juna "kika mareni?" Banza tayi mata tana girgiza hannunta rike da qugu "Adeel ,zama za kayi kana kallon wannan karuwar tana humuliating dina a gabanka?" Maimakon ya bata amsa sai ya sake daukan cup din coffee ya kurba a hankali fuskarsa fal murmushi da annuri "Ƴan mata ,ina da urgent meeting a office a daren nan so bye" ya tashi tsam ya fara tafiya yana zuwa gaban yusra ya tsaya gamida yin qasa da murya "Nasan ke jarumace bari in bar maku gidan ku dambatu kinji ! Ki mata dukan mamaki" yana fadin hakan yayi saɗaf saɗaf ya fice yana guntse dariya kamar tsohon munafuki😂 Hangame baki Yusrah tayi hannunta still dafe da kuncinta. Tana kallo har ya fice,dangas dangas zuby tazo ta gabanta tasa qirjinta ta wani kai mata bangaji ,tayi taga taga zata kifa. "Zo kiyi dambe dani qaramar mara kunya" Ta wuce fuuu tana taku da qarfin izzah ta bar ta yashe cikin rashin madafa a falon Oum Aphnan 09065990265 [6/29, 7:28 AM] Chuchu👻: Washegari Yusrah kwance take tana barci akan gadon ta sai juyi take tana jin dadin barcin ta tun bayan sallah asuba ,bata da niyyar tashi ma . Zuby ne ta shiga dakin a hankali hannunta rike da cup din ruwa ,tana zuwa tsakiyar kanta ta fara tsiyaya mata ruwan sanyin nan a fuska.a gigice yusra ta bude ido cikin haki da tashin hankali take tambayar waye ... Waye... "Dallah tashi ki bamu waje malalaciya ,kina matar aure har qarfe takwas da rabi baki tashi barci ba" "Shine zaki tsiyaya mun ruwan qanqara a fuska ? Kinyi hauka ne? " "Zaki tashi ki taho muje kichen ko sai nayi qasa qasa dake ?" Kafeta da ido tayi tana mamakin ta amma ita ko dage ido ta kalleta ma batayi ba. Na baki minti biyar ki fito kar ki bari in dawo in tardake a gadon nan malalaciya,ta sheko mata sauran ruwan cup din hannunta wani gigif Yusrah tayi gamida jan ajiyar rai itakuwa zuby ,ta wuce fakam fakam ta fice ta banko mata kofa gararam! Sukuti Yusrah tayi wasu irin silent hawaye suka fara silalo mata a fuska Girrrrr ! Wayarta ya soma vibrating ,a sanyaye ta mika hannu don ganin mai kiranta da wannnan duku dukun safen. A sarari ta furta momy sai dai ko ki bazaka iya yi ba saboda yanda Muryar tata ya dushe. "Hello auta ta yakk" Shiru auta ta kasa magana sai hawaye wani na tunkude wani "auta Are You alryt?" Da qyar ta hadiye kukan ta muryarta nadan rawa tace "Yes i am fine momy" "Kinajin dadin zaman kuwa" "Yes" ta bata amsa a takaice saboda kar ta fahimci halin da take ciki "Tom ya Adeel din hope dai yana kula dake sosai" "Sosai da sosai mom ,yana da kirki kuma yana sona " "Uhm that's gud yanzu ina ne zakuje honey moon" Dararas ! Gabanta ya fadi "momy muna dai ta tunani bamu riga mun yanke shawara ba" "Kai har yanzu? You guys arent try at all!...ina Adeel din nasan yana kusa dake sa maganata a speaker" Duddulo ido waje tayi "No momy yana qasa yana haɗa mun abin karyawa ,yana da sona sosai" "Break fast kuma? Ina masu aikinku kuma?" "Momy yace sabon aure baya son mutane suna damunsa maybe sai mun dawo honey moon din sannan" "Oh ohk i missed u my angel" "Nima nayi kewarku sosai momma na " ta qare maganar tana sharce ruwan hawaye "We cant wait to see You back to the office" "Yes mom...I love U" ta fadi a hankali tayi ending call din ta tsaya tayi shiru hannunta rike da wayar "Nine wannan banzar zata watsa ma ruwa? *** Adeel kam yau tunda ya tashi yake neman wasu documents amma ya rasa inda ya watsa in zai iya tunawa tun late wife dinsa nada rai ,kuma in baiyi kuskure ba ita yaba ta ajiye masa lokacin . Wannan yasa ya tafi dakin mamaciyar ya fara fiddo takardunta yana bincika wa ,cike da farinciki yaga doc din da sauri ya fiddo shi a jikin jacket file din ,wani farar takarda ne yaga ya fado ,haka siddan yaji gabansa ya fadi especially ganin rubutun tsohuwar matarsa ,da sauri ya duqa ya dauka ya fara karantawa "Dear my loving husband,Mijina abun alfaharina ina sonka a koda yaushe ,Ina matukar godiya da inganta mun rayuwata da kayi ,Nagode ma Allah da samun nagartaccen miji kamar kai ,thank You For making me mother to be,Allah ya qara haɓɓaka hanyoyin arzikinka ya barrantaka da haram ,ya baka zuriya dayyiba saliha idan akwai rabon aure a tare da kai a gaba Allah ya baka mata saliha wacce ma ta fini komai ,Allah ya jikan iyayenmu Allah ya barmu tare har Aljannah.....Nagode mijina Happy our weeding anniversary 😍" Tun da ya fara karanta wasikar idonsa ya fara tsiyaya da hawaye ya kasa dauke damuwarsa ,tunda ta rasu bai taba mata kuka ba sai yau ,kamar tasan zata rasu take roka mun mace ta gari sai dai kuma kash na samu fankashaliya oh god 😭😭😭 Yusrah kin cuce mu kin cuci Innocent soul baiwar Allah mai riko da addini wacce bata dauki duniya ko arziki a bakin komai ba.... Oum Aphnan 09065990265 [6/29, 12:40 PM] Chuchu👻: Da yanganta da kauɗinta ta shigo dakin kamar an wirgota ,cak ta ja ta tsaya tana kallonsa cikin mamakin ganinsa yana hawaye Cikin rashin kula ,amma dai da dan nuna yanayin zaman tare tace "meke faruwa kuma?" Ɗagowa yayi ya kalleta da jajayen idonsa da sukayi kace kace da hawaye . "Kece zan ma wannan tambayar Yusrah kece..." Sakatoto tayi masa da fuska tana kallonsa ,cikin raunin murya and tremble irin na mai kuka ya sake maimaita "Yusrah duk kece " "Na shiga uku daga tambaya sai cibi ya zama qari Alhaji sha kukan ka ka qoshi ka ga nayi nan" "Dama iyakan abunda zakice kenan tunda kin Koreta kuma kin maye gurbin ta,dama abinda zakice kenan tunda kin kashe ta ....Yusrah me wannan baiwar Allah tayi maki ,mace macen kirki mace ta gari ,naga dai Ni nayi maki laifi tun farkon fari na zubar Maki da magani ,me yasa Ni baza kiyi mun ba sai ki huce akan Innocent wife dina??? Ɗaga murya yayi cikin kuka "shikenan kin kashe ta kinji dadi yusra kin kashe ta!!!" Ji tayi kamar saukan aradu da sauri ta dafe kai ta burkice ta fice a hayyacinta tunda take dashi bata taɓa ganin ya mata tsawa irin hakan ba ,bude baki tayi zatayi magana da sauri ya nunata da takardan hannunsa "Idan kikace tak wallahi sai kinga mummunar matankin da zan dauka a kanki" yana fadin hakan yayi cilli da takardan ya fice a gigice.shiru tayi tana kallon takardan dake yashe a qasa kafin a kasalance ta duka ta dauka ta soma karantawa a hankali cikin zuciyarta. A take taji zuciyarta ta karye tsautsayi da qaddarar zuciya ya Kaita ya barota da duk bata kirata a waya ba da ynz duk hakan

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16