Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 4

Chapter 4

Abban Sojoji 1 Complete Hausa Novel 1,137 words 0 views Progress saved
Download Book

naku "? Jahad tace "Alhamdllh ni da sauki husanna ce abun sai kara gaba yake yi don dr yace koda an mata aikin ba lallai ta dawo yadda ake so ba...." Kuka ne yaci karfinta har takasa karasa maganar , rungumo ta hajjaju tayi a jikinta tana lallashinta " am sorry my daughter stop crying insha Allah everything will be ok , cikin kuka ta amsa da "zandaina mungde ssai ," karasawa Sehrish tayi wurin husanna dake kwance rai hannun Allah , gefen gadon ta zauna tana kallonta idonta cike tab da kwalla tace "Allah ya baki lafiya yar uwata ina jin duk wani irin radadi da kike ji a zuciyarki wanda yayi sanadiyar shigarmu cikin wannan halin bazai taba gamawa da duniya lafiya ba Allah ya isa tsakanin mu dashi mugu azzalumi macuci ..." a karshe ta fashe da kuka ta kwantar da kanta a saman jikinta , har cikin ranta take kukan. Tsohuwar dake kula dasu ce ta shigo cikin sauri hannunta rike da magunguna da takarbo masu , a nan tasamu hajjaju tsaye ita da jahad tana lallashin ta , jin alamar shigowarta yasa suka jiyo suna kallon , cikin sakin fuska tace "Sannun da zuwa hajjaju ke ce da kanki ," murmushi hajjaju tasaki dama sun son juna da alama , " kwarai kuwa nice gwaggo dama ke ce ke rike da yarannan amma ni ban taba ganinsu ba gsky ," murmushi gwaggo tayi tace "bakya leko mune shiyasa amma sun jima wuri na ni nake kula dasu ," jinjina kai hajjaju tayi tace "hakane amma gwaggo jikokinki ne su"? Goggo ta girgiza kai tare da cewa "a'a Allah ne ya hadani dasu nima labari ne mai tsawo , amma ynx bani da kwanciyar hankalin da zan zauna na baki shi , ki bari saina samu natsu," tana gama fadan hakan ta mika ma Jahad magungunan "karbi nan naki ne dakyar nasamu kudi na siyo su," godiya tayi mata ta karba , a tare suka taka izuwa inda sehrish ke kwance jikin Husanna , cike da nuna tsantsar tausayi hajjaju tace "Allah ya bata lafiya Allah sarki mutum baya sanin halin da duniya take ciki wani sa'in sai ziyarci asibiti nan zai ga marasa lafiya iri iri gwanin bantausayi hakika na tausayawa wannan yarinyar tana cikin hali Allah ya kawo musu sauki da duk marasa lafiyan dake fama da ciwo ," amsawa sukayi da amin , har time din sehrish bata dago da kanta ba , ita kadai tasan yadda take ji aranta. Hajjaju ta mayar da idonta kan Gwaggo tace "idan ba damuwa muje ki raka ni wurin likitan zanyi magana dashi ," fita sukayi a tare , wuri Jahad tasamu ta zauna a chair din dake facing din gadon mara lafiyar, kallonsu takeyi su biyun tana kara jin kaunar y'an uwan nata , taji dadin zuwan rishi har cikin ranta , jajircewarta akan ganin sun samu rayuwar mai kyau yana kara mata ninkin son yar uwarta ta, tazama tamkar uwa agare su , alhalin ita age dinsu daya duk da tare suka zo duniya amma sun tsere wa rishi da mintina a wurin haihuwa , tunani iri iri ke zo mata a ranta runtse idonta tayi hawaye na kwaranyo wa daga idonta Gabad'ayansu sun shiga cikin yanayi , duk sunyi zurfin tunani , numfashinta suka soma ji da karfi da karfi wani irin sauti mai matukar razanarwa , a firgice sehrish ta dago da kanta cikin rudu ta furta "Subhanallah! jahad husanna ta cire oxygen da aka samata," a rude jahad ta matso kusa da su hannu tasa ta tana kokarin mayar mata roban oxygen din , buge mata hannu tayi tana wani irin gurnani ga zufa sai ke to mata take yi ga wani irin tari da take yi cikin kuka take ambaton "Seh..seh..sehrish ," Dakyar sound din ke fita , hakan ya tambatar masu da cewa so take tayi ma Sehrish magana amma takasa , matsawa sehrish tayi kusa da ita tare da sa hannu tana shafa mata gefen fuskarta cikin kuka tace "pls husanna kiyi hkr kinji Allah zai baki lafiya , nasan mai kike ji a zuciyarki, zanyi kokari koda zan rasa raina ne wurin ganin kin samu lfy , wlh sai inda karfina ya kare , ina sonki sosai my sister," gaba dayansu kuka sukeyi , mayar mata da roban oxygen din Husanna tayi , bin ta su kayi da kallo ganin tana kokari kakaro murmushi a fuskarta , wani sabon kukan suka sake fashe wa dashi. "Yar'uwata kada ki tafi kibarni ni nafiso na mutu a gabanku dan Allah kada ki tafi ," lokacin da sehrish ta tuna da wannan kalami na Husanna sai jikinta ya kara mutuwa lukus , kamar ba kasusuwa a jikinta, zamewa tayi ta zauna kasan tiles din tare da jingina kanta gefen gadon , wasu abubuwa ta dinga tunawa arayuwarsu wanda in har taci gaba da tuna su to tabbas zuciyata zata buga ne! komai ya dawo masu sabo fal , komawa Jahad tayi ta zauna tana shesshekar kuka hada majina a hancinta , Hannun husanna taji cikin nata , dayake ta aza hannun nata a saman bed din, ta rike shi gam cikin nata , dagowa sehrish tayi da fuskanta wadda tayi jawur , ga idonta sun kada , fuskarta tayi kwaba kwaba cikin kasalalliyar murya tace "Husanna ki daina zubar da hwayenki nasani abun da ciwo , zafinsa yakai kunar wuta amma ki daure pls , ba irin whalar da bansha ba wurin ganin nasamu kudi an miki aikin nan ke da jahad especially ke , kai karshe ma an kokarin bada kaina nayi amma dana tuna abunda mama ta fada saina gaza , duk da haka ban hkr ba na soma kokarin samun wanda zai siye ni yabani kudi kawai na kawo muku ni natafi amma saina tuna cewa in na tafi wazai kula daku ? duk da nasan akwai Allah shine gatan kowane bawansa ...' muryarta ce tashaqe ta gaza idasa maganartata saboda kululun bakin ciki daya tokare mata makoshinta . Jahad da ke sauraron maganar yar uwarta su sai taji wani sabon kukan ya balle mata, domin duk wannan gwagwarmayar da Sehrish tayi sam basu sani ba a boye tayi kayanta. Sun sha kuka kamar ba gobe nima na tayasu kukan duk da bansan takaimaiman tarihin rayuwarsu ba da kuma dalilin kukan nasu. A haka goggo da hajjaju suka same su gwanin ban tausayi , wayar hajjaju dake cikin yar purse dinta sai ringing take yi don haka tace ma serish ta taso su tafi , cikin kuka ta tashi a hankali take tafiya tana waiwayansu , goggo tace " kada ki damu rishi hajjaju ta biya mana kudin gadon kuma tace zata samu koda bashi ne a fara biyan kudin aikin inyaso daga baya kin fara aikin kin samu sai ki biya," Ba karamin dadi sehrish taji ba , haka jahad ma godiya suka shiga yi mata , a karshe tayi masu sallama suka tafi , Har a cikin motan kuka takeyi dakyar hajjaju ta lallashe ta tayi shiru.... Time din da suka dawo , larai na kitchen ita da y'an matan kauyen nan tana koya masu wasu abubuwan daya kamata su sani. A falon suka zauna

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106